Mawaƙa A Idon Hausawa: Ƙorafi A Cikin Waƙar Ranar Mawaƙa Ta Fati Da Kasim
Autor: | Abu-Ubaida Sani, Aliyu Hamma, Ibrahim Aliyu, Kachalla Aliyu Abubakar |
---|---|
Rok vydání: | 2022 |
Předmět: | |
Zdroj: | Scholars International Journal of Linguistics and Literature. 5:209-216 |
ISSN: | 2617-3468 2616-8677 |
DOI: | 10.36348/sijll.2022.v05i07.002 |
Popis: | Hausawa na ɗaya daga cikin al’ummu da Allah ya azurta da ɗimbin mawaƙa. Tun inda aka fito, Bahaushe na amfani da waƙa a kusan dukkan ɓangarori ko al’amuran rayuwarsa. Wannan ya haɗa da sana’o’i (noma da saƙa da dukanci da farauta da sarkanci da ƙira da makamantansu), da kuma zamantakewa da bukukuwa da gyaran muhalli da ma sauran sha’anonin da rayuwar Bahaushe ke ƙunshe da su. Sai dai kamar yadda akan ce; “Idan kiɗa ya canza, rawa ma sai ta canza,” haka ma siga da salon waƙoƙin Hausa na canzawa tare da canjin zamani. A yau zamani ya kai, an samu mawaƙa da dama da ke amfani da kayan kiɗa na zamani yayin rera waƙoƙinsu. Sai dai wani abu shi ne, mawaƙan ƙasar Hausa na fuskantar tsangwama. Sau da dama matsayinsu ga idon jama’a ba ya wuce maroƙa ko limamen shashanci. Wannan ne ya sanya mawaƙa da dama ke rera waƙoƙi da ke nuna ƙorafinsu ga hakan. Wannan takarda ta nazarci ɗaya da cikin waɗannan waƙoƙi mai suna Waƙar Ranar Mawaƙa wanda Fati da Kasim suka rera. Sakamakon nazarin na nuna cewa; mawaƙa na fuskantar tsangwama a ƙasar Hausa. Sannan al’umma ba ta tallafa wa waɗannan mawaƙa ta fuskar shawarwari da sauran abubuwa da suka dace. Daga ƙarshe an ba da shawarwari da suka haɗa da, a riƙa jawo mawaƙa jiki tare da ƙarfafa musu guiwa da nusar da su kan samar da waƙoƙi masu amfani ga al’umma ta fuskar ilimi da zamantakewa. |
Databáze: | OpenAIRE |
Externí odkaz: |